Duba duk katunan da aka fi kallo a Noor Gallery ..
Kalli katikan yabawar kullum
Kauracewa ba ta nufin mantawa kawai... A’a tana nufin mu rayu amma kamar Alqur’ani bai damemu ba. #Kada_Kaurace masa
Ka suranta a kai sunanka cikin wadanda manzonka ya kai kararsu... Saboda kawai ka kaurace wa littafin Allah. #Komawa_Zuwa ga_Alqur’ani
Idan ka samu zuciyarka a halarce a yayin karanta wata aya... To kana kusa da abin da kake tsammani #Ka saurara_da zuciyarka.
Alqur’ani ba ya zuwar maka da wani tunani da za ka warware shi, a’a sai dai shi kamar boyayyan sauti ne da yake raya abin da ka yi zaton ya mutu a zuciyarka. #Sautin_Alqur’ani
Shan wahala ba shi ne rasa hanya ba... A’a shan wahala yana cikin dogewa a kan hanya tare da yin nisa ga hasken shiriya...kuma da sannu da za ka samu nutsuwa.. #Hutun_Alqur’ani
Dukkanin hanyoyi za su iya batar da kai, Ban da hanya kwaya daya...Allah ne ya rubutata da kansa: To duk wanda ya bi shiriyata ba zai tave ba, kuma ba zai wahala ba”. #Hanyar_Allah
Ba sharadi ba ne sai ka fahimci komai. Ya isheka kawai ka bude zuciyarka...Allah ya sawwake littafinsa ga wanda ya ga dama. #Haske_Ga wanda_Ya neme shi
Kada ka ce: “Akwai wahala”. Hakika Allah ya yassare shi...ba don a karanta shi ba kawai, a’a don ya taba zuciyarka. Ka fara....tafiyar za ta ba ka mamaki #Hanyar_Alqur’ani
Kowace aya ta sauka ne don isa zuwa ga zuciyarka... Kuma dukkan wani wa’azi da ke cikinsa ....kamar an rubuta shi ne don kai kadai. #Sako_Na Musamman
A’a bayani ne da shiriya ga wanda zuciyarsa ta rayu don gaskiya. #Muryar_Gaskiya
Ya isheka ka san cewa a gaba gareka akwai wani littafi daga Allah... Wanda yake cike da gaskiya da rahama da bayani. #Zancen_Allah
Wani lokacin baka bukatar amsa....sai dai haske. To hakika haske ya zo maka daga Allah wanda zai cika zuciyarka da nutsuwa. #Hasken_Alqur’ani