Duba duk katunan da aka fi kallo a Noor Gallery ..
Kalli katikan yabawar kullum
Bayan an gama hayaniyar...to mutum zai zamana shi kaxai daga shi sai zuciyarsa. To a nan ne tambayoyi na gaskiya suke farawa. #Hasken_Alqur’ani#Bayan_wasa#Gaskiya#Hasken_Alqur’ani#Nutsuwar_Zuciya
Shahara...tafi...haske...dukkansu abubuwa ne da suke tafiyar da fadakuwar mutum cikin sauri. Sai dai kuma ba sa cika ruhi da abin da yake buqata koda yaushe.
“Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa”.
Yayin da ake cikin kaxaici ko damuwa...Alqur’ani yana magana game da kusancin Allah ga mutum. #Hasken_Alqur’ani#Imani#Saqon_Alqur’ani#Zuciyar_xan’adam#Qwallon_qafar_duniya.
Miliyoyin mutane suna kallon gasa-gasa a wurare mabambanta... sai dai mutum yana da buqatuwa zuwa ga wanda zai saurare shi ya fahimce shi da gaskiya.
“Kuma Shi Yana tare da ku a duk inda kuka kasance”. [Hadid: 4]
Alqur’ani yana tunatar da mutum wani abu da yake mantawa da shi yayin da yake tsaka a cikin wasu shagulgula: lallai tafiyar gajera ce...kuma ma’anar abu ta fi hayaniya muhimmanci.#Hasken_Alqur’ani#Mahanga#Tafiyar_rayuwa#Kofin_duniya#Musulunci
Kowace irin jarumta tana da qarshe. Hakanan ita ma rayuwa tana da qarshe.
“Sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku”. [Sajda: 11]
Wasu nasarorin ba sa zuwa da gaggawa. Hakanan yayin da ake rayuwa, haquri wani yanki ne na tafiyar da ake kan yinta. #Hasken_Alqur’ani#Haquri#Imani#qwallon_qafa#Ayar_Alqur’ani
Mutane suna girmama xan wasan da ba ya sarewa ya miqa wuya. Hakanan shi ma Alqur’ani yana koyar da mutum yadda zai jure ya yi haquri ya ci gaba da bin hanya.
“Lalle Allah Yana tare da masu haquri”. [Baqara: 153]