“Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa”.
Nuna katika
Mutane suna girmama xan wasan da ba ya sarewa ya miqa wuya. Hakanan shi ma Alqur’ani yana koyar da mutum yadda zai jure ya yi haquri ya ci gaba da bin hanya.
Kowace irin jarumta tana da qarshe. Hakanan ita ma rayuwa tana da qarshe.
Yayin da ake cikin kaxaici ko damuwa...Alqur’ani yana magana game da kusancin Allah ga mutum. #Hasken_Alqur’ani#Imani#Saqon_Alqur’ani#Zuciyar_xan’adam#Qwallon_qafar_duniya.
Shahara...tafi...haske...dukkansu abubuwa ne da suke tafiyar da fadakuwar mutum cikin sauri. Sai dai kuma ba sa cika ruhi da abin da yake buqata koda yaushe.
Miliyoyin mutane suna kallon gasa-gasa a wurare mabambanta... sai dai mutum yana da buqatuwa zuwa ga wanda zai saurare shi ya fahimce shi da gaskiya.
Alqur’ani ba ya ganin mutum a matsayin wasu lambobi kawai a wannan duniyar. Sai dai yana ganinsa a matsayin abin halitta mai manufa kuma mai xauke da wani saqo.#Hasken_Alqur’ani#Manufa#Ma’anar_rayuwa#Alqur’ani#Kofin_duniya