Duba duk katunan da aka fi kallo a Noor Gallery ..
Kalli katikan yabawar kullum
Shiriya tana farawa lokacin da zuciya ta fuskanto wa shiriya da gaskiya, ba lokacin da aka gama fahimta ba. #Shiriya
Alqur’ani ba ya barinka a tsakiyar hanya, sai dai yana kasancewa tare da kai har sai ka samu nutsuwa. #Nutsuwar_Alqur’ani.
Babu wata buqata da zuciya take da ita face Alqur’ani ya yi bayani game da ita ko kuma ya ba da wata shiriya ko ya kawo rahama game da ita. #Shiriya_Da Rahama.
Alqur’ani ba ya yi wa duhu ado, sai dai ma ya fitar da kai daga duhu, mataki bayan mataki. #Hasken_Yaqini.
Saqon Alqur’ani ba canja matashiyoyi ba ne, sai dai saqon Alqur’ani tseratar da mutum ne daga ximuwa. #Saqon_Alqur’ani
Yayin da tambayoyi suka yi cincirindo, to ba ka buqatar hayaniya a lokacin, sai dai kana buqatar hasken da zai yi maka jagora cikin nutsuwa. #Hanyar_Gaskiya
Alqur’ani ba shiryayyiyar amsa ba ce ba kawai, sai dai haske ne da yake abokantakarka, lokacin da kake can kana laluben wani abu. #Hasken_Shiriya
Yayin da Allah zai so ka, to za ka samu tabbatuwa, ba za ka ji tsoron zargi ba, ba kuma za ka siyar da gaskiya da ka sani ba. #Tabbatuwar_Imani
Mafi girman matsayin da mutum zai samu shi ne Allah ya so shi tun kafin shi ya so Allah. #Yana sonsu_Su ma Suna sonshi
Ba kowane abin da ake so ne ake yin fafutuka a same shi ba, wata karvuwar kyauta ce daga Allah. #Soyayya_Daga_Allah.
Yayin da ka so Allah da gaske, to baka buqatar neman mutane su so ka, domin Allah Mai rahama zai dasa musu qaunarka a zukatansu yadda baka tsammani. #Qaunar_Allah Mai Rahama
Son Allah ba da’awa ba ce, sai dai zavi ne da yake canja abubuwan da aka fifita ya ‘yantar da zuciya daga rataya kanta da abin da yake ba na gaskiya ba. #Zuciya_Da Imani