Rayuwa takaitacciya ce duk yadda kuwa ta yi tsayi. Babban abin nema ba a cikin qawar duniya yake ba, a’a yana cikin makomar da babu matsera daga gareta. Ka tuna cewa mafi girman yaudara shi ne ka shagala da xan abin da yake da lokaci kankani a kan mai lokaci dawwamamme.
Ya ku mutane, lalle alqawarin Allah gaskiya ne, saboda haka kada rayuwar duniya ta ruxe ku; kada kuma mai ruxarwa (Shaixan) ya ruxe ku game da Allah. Lalle Shaixan maqiyinku ne, saboda haka sai ku riqe shi maqiyi. Lalle yana kiran mutanensa ne don su zama ‘yan wuta. [Faxir: 5-6]

Maqiyi na hakika ba shi ne wanda yake husuma da kai a kan duniya ba, a’a maqiyi na hakika shi ne wanda yake so ya vatar da kai daga bin hanyar Allah. Kiyaye wannan zai canja maka muhimman abubuwanka su ci gaba, ya kuma tsare zuciyarka daga gafala.
Haqiqa waxanda suka qaryata haxuwa da Allah sun yi hasara; har sai lokacin da alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, sai su ce: “Kaiconmu kan irin sakacin da muka yi a cikinta (duniya),” alhalin kuwa suna xauke da kayan laifukansu a bayansu. Ku saurara, abin da suka xauka na laifi ya munana matuqa. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face wasa da sharholiya; kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba? [An’am: 31-32]
Mafi hatsarin hasara shi ne rayuwa ta qare a cikin gafala, sai daga baya mutum ya gane hakan. Nadama ba ta amfani a ranar alkiyama. Don haka daga yau ka fara yin abin da zai tseratar da kai gobe.
Haqiqa waxanda suka qaryata haxuwa da Allah sun yi hasara; har sai lokacin da alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, sai su ce: “Kaiconmu kan irin sakacin da muka yi a cikinta (duniya),” alhalin kuwa suna xauke da kayan laifukansu a bayansu. Ku saurara, abin da suka xauka na laifi ya munana matuqa. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face wasa da sharholiya; kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba? [An’am: 31-32]
Duk yadda duniya ta ruxeka, tana nan a matsayinta na abar wargi da wasa. Amma samun dacewa mai wanzuwa na wanda ya rayu da taqawa ne, kuma zai fahimci cewa bin hanya zuwa ga Allah shi ne abin nema na gaskiya.
Ku sani cewa, ita dai rayuwar duniya ba wata aba ba ce sai wasa da sharholiya da qyale-qyale da kuma fariya a tsakaninku da takara wajan nuna yawan dukiya da ‘ya’yaye; ta yi kama da ruwan saman da tsirransa suka bai wa manoma sha’awa, sannan duk ya bushe, sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan kuma ya zama dudduga; a lahira kuwa akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin daxi mai ruxi. [Hadid: 20]
Qyale-qyalen duniya yana kama da shukar da take qawatar da ido na xan lokaci, sannan ta zagwanye cikin sauri. Kada ka sanya rayuwarka cikin abin da zai gushe nan da nan, ka nemi abin da zai wanzu bayan mutuwarka.
Ku sani cewa, ita dai rayuwar duniya ba wata aba ba ce sai wasa da sharholiya da qyale-qyale da kuma fariya a tsakaninku da takara wajan nuna yawan dukiya da ‘ya’yaye; ta yi kama da ruwan saman da tsirransa suka bai wa manoma sha’awa, sannan duk ya bushe, sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan kuma ya zama dudduga; a lahira kuwa akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin daxi mai ruxi. [Hadid: 20]
Mutum yana tsakanin hanyoyi guda biyu: Jin daxi na dan lokaci da zai shagaltar da zuciya, ko kuma gafara da yardar da ba ta gushewa. Ka tambayi kanka, wace hanya za ka zava cikin hanyoyin nan.
Ya ku waxanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zace-zace, lalle shashin zace-zace laifi ne; kada kuma ku riqa binciken laifukan wasu, kuma kada shashinku ya riqa gibar shashi. Yanzu xayanku zai so ya ci naman xan’uwansa matacce? To sai kuka qi shi. To ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai karvar tuba ne, Mai jin qai. [Hujurat: 12]
Samun bambanci tsakanin mutane a launi da asali ba shi ne sababi na samun fifiko a tsakanin mutane ba, ko sababin bambanci a tsakaninsu ba, a’a kawai dai hanya ce da aka sanya don samun haxin kai. Daraja ta haqiqa tana cikin tsaftar zuciya da kiyaye dokokin Allah.
Ya ku waxanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zace-zace, lalle shashin zace-zace laifi ne; kada kuma ku riqa binciken laifukan wasu, kuma kada shashinku ya riqa gibar shashi. Yanzu xayanku zai so ya ci naman xan’uwansa matacce? To sai kuka qi shi. To ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai karvar tuba ne, Mai jin qai. [Hujurat: 12]
Nasabar mutum ko dukiyarsa ko yanayin halittarsa ba shi yake xaga darajar mutum ba, abin da zai daga darajarsa shi ne gaskiyarsa tare da Allah da kiyaye dokokin Allah. Ma’aunin sama ya saba da ma’aunan kasa.
Wancan gida na lahira Muna ba da shi ga waxanda ba sa nufin girman kai da varna a bayan qasa. Kyakkyawan qarshe kuma yana ga masu kiyaye dokokin Allah ne. Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waxanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa. [Qasas: 83-84
Gidan dawwama ba na masu girman kai ba ne ko mavarnata, sai dai shi na wanda ya qanqan da zuciyarsa ne ya kiyaye dokokin Ubangijinsa. A nan ne ake gane haqiqanin matsayai.
Wancan gida na lahira Muna ba da shi ga waxanda ba sa nufin girman kai da varna a bayan qasa. Kyakkyawan qarshe kuma yana ga masu kiyaye dokokin Allah ne. Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waxanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa. [Qasas: 83-84
Ma’aunin lahira na adalci ne: Kyakkyawan aiki yana bayuwa zuwa ga alheri mafi girma. Mummunan aiki kuma ba a saka wa wanda ya yi shi face da abin da ya aikata. Damarka ta yau ita ce ka zava wa kanka abin da za ka yi guzuri dashi a gobe qiyama.
Kuma kada ku auri wadda iyayenku maza suka aure ta cikin mata, sai fa abin da ya riga ya shuxe. Lalle yin hakan ya kasance alfasha ce kuma abu ne da zai jawo fushin Allah, kuma tafarki ne wanda ya yi muni. An haramta muku auren iyayenku mata da ‘ya’yanku mata da ‘yan’uwanku mata da gwaggonninku da yagwalgwalanku da ‘ya’yan xan’uwa da ‘ya’yan ‘yar’uwa da iyayenku waxanda suka shayar da ku da ‘yan’uwanku mata ta wajen shayarwa, da iyayen matanku da agololinku waxanda suke cikin gidajenku, waxanda matan da kuka tava saduwa da su suka haife su, in kuwa ba ku tava saduwa da su ba, to babu laifi a kanku, da matan ‘ya’yanku maza waxanda suke na tsatsonku; haramun ne kuma ku haxa ‘yan’uwa mata biyu, sai dai abin da ya wuce a baya. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai jin qai. [Nisa’i: 22- 23]
Musulunci bai bar alaqoqi su riqa tafiya haka kawai ba tare da qa’idoji ba, a’a ya sanya shinge da zai kare iyali daga rugujewa, ya kuma kare tsatso da darajar ‘yan’adamtaka.
Kuma kada ku auri wadda iyayenku maza suka aure ta cikin mata, sai fa abin da ya riga ya shuxe. Lalle yin hakan ya kasance alfasha ce kuma abu ne da zai jawo fushin Allah, kuma tafarki ne wanda ya yi muni. An haramta muku auren iyayenku mata da ‘ya’yanku mata da ‘yan’uwanku mata da gwaggonninku da yagwalgwalanku da ‘ya’yan xan’uwa da ‘ya’yan ‘yar’uwa da iyayenku waxanda suka shayar da ku da ‘yan’uwanku mata ta wajen shayarwa, da iyayen matanku da agololinku waxanda suke cikin gidajenku, waxanda matan da kuka tava saduwa da su suka haife su, in kuwa ba ku tava saduwa da su ba, to babu laifi a kanku, da matan ‘ya’yanku maza waxanda suke na tsatsonku; haramun ne kuma ku haxa ‘yan’uwa mata biyu, sai dai abin da ya wuce a baya. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai jin qai. [Nisa’i: 22- 23]
Abin da Allah ya haramta cikin abin da ya shafi auratayya, ba haramtawa ba ce kawai, a’a ba da tsaro ne da kuma rahama, ta yadda za a samu tsarkakakkar dangantaka da tabbatattun gidaje da amintacciyar al’umma.
Haka ma da matan aure, sai dai qwaraqwaranku; wannan hukuncin Allah ke nan a kanku. Kuma an halatta muku (sauran) matan da ba waxannan ba, ku neme su da kuxinku, kuna masu kame kanku, ba ma su zina ba. To waxanda kuka sadu da su daga cikinsu ku ba su sadakinsu wanda kuka yanka musu. Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi yarjejeniya da shi bayan sadakin da kuka yanka. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima. [Nisa’i: 24]
A Musulunci, aure ya ginu ne a kan tsarki da mutuntawa, ba a kan wargi da sha’awar da za ta zo ta wuce ba. Aure wani alkawari ne, kuma wani nauyi ne da yake tsare matsayi yake kuma kiyaye hakkoki.
Haka ma da matan aure, sai dai qwaraqwaranku; wannan hukuncin Allah ke nan a kanku. Kuma an halatta muku (sauran) matan da ba waxannan ba, ku neme su da kuxinku, kuna masu kame kanku, ba ma su zina ba. To waxanda kuka sadu da su daga cikinsu ku ba su sadakinsu wanda kuka yanka musu. Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi yarjejeniya da shi bayan sadakin da kuka yanka. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima. [Nisa’i: 24]
A Musulunci ana gina alakoki a kan yarda da adalci, ba a kan abin da za a samu ko hayaniya ba, abin da aka ba da a matsayin sadaki, shi ne lamunin kiyaye hakkokin mace da tabbatuwar iyalai.
“Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini, kuma kun yi sallama ga masu su. Wannan kuwa shi ya fi alheri a gare ku don ku wa’azantu. To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne. [Nur: 27-28]
Gidaje ba katangogi ba ne kawai, a’a wurare ne na samun aminci da hutu ga masu su. Saboda haka ne ma Musulunci ya sanya neman izini ya zama aminci da zai kiyaye sirri ya kuma dasa mutuntawa.
“Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini, kuma kun yi sallama ga masu su. Wannan kuwa shi ya fi alheri a gare ku don ku wa’azantu. To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne. [Nur: 27-28]
Kwankwasa kofa cikin ladabi, da komawa yayin da ba a ba da izinin shiga ba, ba rauni ba ne, a’a tsarkake rai ne da gina al’ummar da za ta ginu a kan kunya da mutuntawa.
Ya ku waxanda suka yi imani, bayinku da kuma waxanda ba su isa mafarki ba a cikinku (watau waxanda ba su balaga ba) su nemi izininku sau uku. Kafin sallar Asuba da sanda kuke tuve tufafinku a lokacin garjin rana da kuma bayan sallar Lisha. Lokatai ne guda uku na tsiraicinku. Babu laifi a kanku ko a kansu bayansu (waxannan lokatai). Masu shige da fice ne a gare ku sashinku bisa sashi. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi. Allah kuma Masani ne, Mai hikima. [Nur: 58]
Musulunci ya koyar da mu cewa, gidaje suna da lokuta na musamman, wanda har qananun yara ana tarbiyantarsu a kan girmama su. Ladabi ne kankani amma zai samar da al’umma tsaftatacciya mai kunya da kiyaye shamakin da aka sa mata
Ya ku waxanda suka yi imani, bayinku da kuma waxanda ba su isa mafarki ba a cikinku (watau waxanda ba su balaga ba) su nemi izininku sau uku. Kafin sallar Asuba da sanda kuke tuve tufafinku a lokacin garjin rana da kuma bayan sallar Lisha. Lokatai ne guda uku na tsiraicinku. Babu laifi a kanku ko a kansu bayansu (waxannan lokatai). Masu shige da fice ne a gare ku sashinku bisa sashi. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi. Allah kuma Masani ne, Mai hikima. [Nur: 58]
Tsara neman izini a lokutan hutu ba bayani ne da ya zo daga baya ba, a’a wata hikima ce ta Ubangiji, don tsare mutuncin iyalai, a kuma tarbiyance su a kan tsarkaka da mutuntawa.
Idan kuma yara daga cikinku suka isa mafarki (watau suka balaga) sai su nemi izini kamar yadda waxanda suke gabaninsu suka riqa neman izini. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. [Nur: 59]
Tarbiyantar yara qanana a kan neman izini daga lokacin da suka balaga, tana sa jin kunya ya zama tabbatacciyar al’ada a gare su. Kuma hakan yana kare gidaje daga zama na hayaniya, kuma yana dasa mutuntawa a cikin rayuka.
Idan kuma yara daga cikinku suka isa mafarki (watau suka balaga) sai su nemi izini kamar yadda waxanda suke gabaninsu suka riqa neman izini. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. [Nur: 59]
Neman izini ba wani yanayi ba ne na zaman tare ba kawai, a’a tarbiya ce ta imani da take koyar da ‘ya’ya yadda za su mutunta abubuwan da suka shafi wasu tun suna yara kanana.