(Ka tuna) ranar da za ka ga muminai maza da muminai mata haskensu yana tafiya ta gabansu da ta damansu, (ana cewa da su): “Albishirinku a wannan rana (su ne) gidajen Aljanna da qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma.”
A ranar da munafukai maza da munafukai mata za su riqa cewa da waxanda suka yi imani: “Ku saurara mana mu xan xosani haskenku.” Aka ce (da su): “Ku koma bayanku (watau duniya) sai ku nemi haske.” sai aka raba tsakaninsu da katanga wadda take da wata qofa, daga cikinta akwai rahama, bayanta kuma azaba ce (take bugowa) daga gare ta
Katika masu alaka
Nuna katika
