Haqiqa wanda ya tsarkake shi (ran) ya rabauta
Haqiqa kuma wanda ya binne shi da savo ya tave
Nuna katika
Neman tsari daga Allah yana kore shetan kuma yana ƙarfafa zuciyarka. Ka yawaita maimaita shi domin zuciyarka ta zauna lafiya.#Garkuwar_Mumini #Ambaton_Allah
Komai dabarar shaidan, tana da rauni a gaban wanda ya nemi taimakon Allah. Kada ka ji tsoro, ka kasance tare da Allah koyaushe. #Dabarar_Shaitan #Dawwamani
Lalle Allah ba Ya zalunci ko da daidai da nauyin jaririyar tururuwa; kuma idan ya kasance aiki ne mai kyau to zai ninka shi, kuma Ya ba da lada mai girma daga wurinsa
Ayat al-Kursi: Mabudin tsira daga shaidan kuma garkuwa ga mumini. Karanta ta kowace safiya da maraice, domin ita ce mafi girman aya a cikin Alqur'ani Mai Girma. #Ayat_al_Kursi #Girman_Allah
Haqiqa kuma Mun halicci mutum, kuma Mun san abin da ransa yake saqa masa; kuma Mu Muka fi kusa da shi fiye da jijiyar wuyansa
Ka ce (da su): “Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karvi ranku sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku