Biyu xin nan (muminai da kafirai) masu jayayya ne da suka yi jayayya game da Ubangijinsu (wato addininsu); waxanda suka kafirce sai aka xinka musu tufafi na wuta, kuma ana zuba musu tafasasshen ruwa ta saman kawunansu(20)Ana narka abin da yake cikinsu da shi (tafasasshen ruwan) da kuma fatu(21)Suna kuma (shan duka) da gudumomi na baqin qarfe(22)Duk sanda suka yi nufin fita daga cikinta (wutar) saboda baqin ciki sai a sake mayar da su cikinta, (a ce da su): “Ku xanxani azabar gobara.”
Katika masu alaka
Nuna katika