Da kuma masu rige-rige (zuwa alheri (11)Waxannan su ne makusanta(12)A cikin gidajen Aljanna na ni’ima(13)Su jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummun) farko(14)Kuma kaxan ne daga (al’ummun) qarshe(15)Suna kan gadaje masu adon zinari(16)Suna kishingixe a kansu suna fuskantar juna(17)Yara samari dawwamammu (masu hidima) za su riqa zagaya su(18)Da kofuna (marasa mariqai) da butoci masu hannaye da kuma qoquna na giya(19)Ba sa ciwon kai saboda ita, kuma ba sa buguwa(20)Da kuma ababan marmari na abin da suke so su zava(21)Da kuma naman tsuntsaye na abin da suke sha’awa(22)Da kuma matan Hurul-Ini
(23)Kamar misalin lu’ulu’u da yake cikin kwasfa(24)Sakamako ne na abin da suka kasance suna aikatawa(25)Ba sa kuma jin wani zancen banza da mai sa zunubi a cikinta(26)Sai dai faxar salamun-salamun[1](27)Ma’abota hannun dama kuwa, mamakin darajar ma’abota hannun dama!(28)Suna cikin ‘ya’yan itacen magarya marasa qaya(29)Da kuma ayaba mai ‘ya’ya dava-dava
(30)Da inuwa madawwamiya (31) Da kuma ruwa mai kwarara
(32)Da ababen marmari masu yawa(33)Ba masu yankewa ba kuma ba ababen hanawa ba(34)Da shimfixu masu daraja(35)Lalle Mu ne Muka qage su (‘yan matan Aljanna) sabuwar qagowa(36)Sannan Muka sanya su budurwai(37)Masu begen mazajensu, tsarekun juna
(38)Don ma’abota hannun dama(39)Su jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummun) farko(40)Kuma jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummar) qarshe
Katika masu alaka
Nuna katika