Abubuwan da Gaskiya da Shiriya Suka Kebanta dasu

Abubuwan da Gaskiya da Shiriya Suka Kebanta dasu

Abubuwan da Gaskiya da Shiriya Suka Kebanta dasu

92 36


A Alqur’ani Allah (SWT) yana amfani da ba da misalai a matsayin gadoji da za su hada tsakanin fahimtar dan’adam da wasu abubuwa da Allah yake so ya tabbatar. “Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komai qanqantarsa, sauro da abin ya fi shi....” [Baqara: 26]. Wannan ayar tana tunatar da mu cewa babu wani abu a cikin halittun Allah da yake qarami ko wanda ba shi da muhimmanci da kuma nuna cewa, za a iya fitar da hikima hatta a cikin sassauqan halittun Allah. Misalan da Allah yake ba da wa a cikin Alqur’ani suna koyar da mu yin tuntuntuni game da halittun Allah don daukar izina da darussa wadanda za su karfafa mana imaninmu su kuma haska mana hanyar da za mu bi mu samu shiriya.

Misalan Alqur’ani suna nuna kyawu da girman Allah mahalicci, suna kuma bayyana yadda imani yake zurfafa fahimtarmu yake kuma yi mana jagora zuwa ga fahimtar gaskiya daga Ubangijinmu.

Wadannan misalan suna gabato wa da Muminai basira da haske. Yayin da a gefe guda suke bayyana wa kafirai rashin ikonsu a kan fahimtar wata haqiqa ta Ubangiji saboda nisan su da imani.

Wadannan misalan ba wai labarai ba ne kawai ko wasu abubuwa da za a hada a tsakanin wani da wani, a’a darussa ne na rayuwa da suke koyar da mu ya ya za mu rayu ta hanyar da za ta yardar da Allah ta kuma tabbatar mana da alheri garemu da wasunmu.

Allah (SWT) yana amfani da ba da misalai don ya gwada fahimtarmu da kuma imaninmu, don ya bayyana bambancin da ke tsakanin masu yin tuntuntuni game da ayoyinsa da koyonsu da kuma masu bijire musu. A kowane misali da aka ba da akwai kira zuwa ga yin tuntuntuni da lura, domin mu yi duba mu ga yadda Allah yake fuskantar da mu zuwa ga gaskiya da abin da yake daidai.

Misalan da Alqur’ani yake bugawa suna dauke da rahama da shiriya ga wanda ya yi tuntuntuni game da su ya kuma rayu bisa kan abin da suke hukuntawa.

Ku barmu mu sanya Alqur’ani da misalansa su zama masu shiryarwa a gare mu a cikin kowane taku daga cikin matakan rayuwar mu. Mu yi tuntuntuni game dasu da budaddun zuciyoyi da hankula masu kiyayewa, don mu yi rayuwa tare da hikima da imani.

Ko da yaushe mu riqa tunawa cewa, Allah ba ya jin kunyar bayyana gaskiya, da tuna cewa, a kowane misali daga cikin misalan da yake ba da wa akwai kira na gaskiya na yin tuntuntuni da yin tadabburi game da girman halittarsa da hikimarsa.

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya