Qaqqarfan misali a cikin Suratul Baqara yana bayyana tare da siffanta halin wanda yake neman shiriya ba tare da gaskiya wurin neman ba ko riqo da ita (gaskiyar) ba. Allah Ta’ala yana cewa: “Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala har ya kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani. Wannan misalin yana nuna halin wanda yake ganin gaskiya a bayyane a lokaci guda – kamar haske ne yake haskakawa a gefensa – amma nan da nan sai ya rasa wannan hasken saboda raunin imaninsa ko saboda juyawar zuciyarsa, don haka sai shiriya ta bar shi ya koma zuwa ga duffan jahilci da bata, ba tare da ya samu damar ganin ingantacciyar hanya ba. Bari mu yi tuntuntuni game da wannan misalin mu dauki izina yayin da muke neman haske na haqiqa, watau hasken imani da yaqini da Allah. Mu sanya zukatanmu su yi riqo da shiriya, su zama cikin shiri na tafiya da tabbata a kan tafarki madaidaici. Hasken da Allah ya ke shiryar da wanda ya ga dama da shi daga cikin bayinsa, wajibi ne mu neme shi da gaske da kuma ikhlasi, kada mu bar shi ya kufce mana, a’a mu kiyaye shi ta hanyar yin ayyuka na na gari da kuma neman kusancin Allah. Ku kasance masu neman haske yayin da ake cikin duffan rayuwa, shi ne hasken nan da ba ya bicewa, watau hasken shiriya da Alqur’ani da sunnah, don su haska mana hanya su kuma shiryar damu a kowane taku. Hasken da ke cikin zukatanmu shi ne basirar da muke ganin gaskiya da ita, muke kuma tafiya a kan ta bisa aminci da imani. |
Katika masu alaka
Nuna katika