Yanci ba shi ne ka faxi abin da ka ga dama ba. ‘Yanci shi ne ka faxi gaskiya ba tare da jin tsoro ko son zuciya ba
Biyayya ga Allah ba dabaibayi ba ce, sai dai ita hanyar rabauta ce mai girma.
Yanci a cikin Alkur'ani
Ka miqa kanka ga Allah kana mai biyayya a gare shi shi ne mafi qololuwar ‘yanci. Saboda kana zava wa kanka hanyar aminci ne bisa zavinka.
‘Yantacce shi ne wanda ya tsarkake zuciyarsa ga Allah ba ga mutane ba
Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku faxi Magana wadda take daidai ce. Zai kyautata muku ayyukanku, Ya kuma gafarta muku zunubanku. Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa, to haqiqa ya rabauta rabauta mai girma. [Ahzab: 70-71]
‘Yanci ba shi ne ka faxi abin da ka ga dama ba. ‘Yanci shi ne ka faxi gaskiya ba tare da jin tsoro ko son zuciya ba.
Magana ta daidai ita ce, sautin zuciya wanda yake kiyaye dokokin Allah kafin ya furta magana.
Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku faxi Magana wadda take daidai ce. Zai kyautata muku ayyukanku, Ya kuma gafarta muku zunubanku. Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa, to haqiqa ya rabauta rabauta mai girma. [Ahzab: 70-71]
Duk wanda ya qanqantar da kansa ga Allah, to zai ‘yantu daga bautar dukkan wani wanda ba Allah ba.
Biyayya ga Allah ba dabaibayi ba ce, sai dai ita hanyar rabauta ce mai girma.
To ku gudo zuwa ga Allah, lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi). Kada kuma ku sanya wani abin bauta tare da Allah; lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi). [Zariyat: 50-51]
Samun ‘yanci na gaskiya shi ne ka gudo daga bautar duniya zuwa ga rahamar Allah, Allah ya ce, “To ku gudo zuwa ga Allah”. Gudowar ‘yantattu ba ta kasancewa sai zuwa gare shi.
To ku gudo zuwa ga Allah, lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi). Kada kuma ku sanya wani abin bauta tare da Allah; lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi). [Zariyat: 50-51]
Duk wata mafaka da za a samu daga wanin Allah, to wata voyayyiyar shamaki ce ga barin saduwa dashi, hakanan duk wani kaxaita Allah da bauta da za a yi, to komawa zuwa gare shi ne na har abada.
Kada ka kuskura ka sanya abin bauta tare da Allah. Idan ka yi haka, to za ka zamo bawa ‘yantacce na gaskiya.
Wanda kuma ya miqa kansa ga Allah, yana kuma mai kyautatawa, to haqiqa ya yi riqo da igiya qwaqqwara. Kuma qarshen al’amura zuwa ga Allah ne. Duk kuwa wanda ya kafirta, to kada kafircinsa ya vata maka rai. Zuwa gare Mu ne kawai makomarsu take, sai Mu ba su labarin abin da suka aikata. Lalle Allah Masanin abin da yake cikin qiraza ne.” [Luqman: 22-23]
Ka miqa kanka ga Allah kana mai biyayya a gare shi shi ne mafi qololuwar ‘yanci. Saboda kana zava wa kanka hanyar aminci ne bisa zavinka.
‘Yantacce shi ne wanda ya tsarkake zuciyarsa ga Allah ba ga mutane ba.
Wanda kuma ya miqa kansa ga Allah, yana kuma mai kyautatawa, to haqiqa ya yi riqo da igiya qwaqqwara. Kuma qarshen al’amura zuwa ga Allah ne. Duk kuwa wanda ya kafirta, to kada kafircinsa ya vata maka rai. Zuwa gare Mu ne kawai makomarsu take, sai Mu ba su labarin abin da suka aikata. Lalle Allah Masanin abin da yake cikin qiraza ne.” [Luqman: 22-23]
Duk wanda ya miqa kansa ga Allah, to jujjuyawar lamarin rayuwa ba zai girgiza shi ba, hakanan kafircin kafirai ma ba zai girgiza shi ba.
‘Yanci na gaskiya shi ne ka san cewa makoma gare shi take shi kaxai.
Kuma ka ce: “Gaskiya daga Ubangijinku take;” to wanda ya ga dama ya yi imani, wanda kuma ya ga dama sai ya kafirta. Lalle kam Mun tanadar wa azzalumai wata wuta wadda katangarta ta kewaye su. Idan kuma suka nemi taimako to za a taimake su ne da ruwa kamar tafasasshen mai da zai riqa toye fuskoki. Tir da wannan abin shan makoma kuma ta munana.” [kahfi: 29]
Musulunci ba ya tilastawa sai an yi imani, sai dai yana bijirar da gaskiya a fili ta bayyana: Allah ya ce, “To wanda ya ga dama ya yi imani, wanda kuma ya ga dama sai ya kafirta.”
‘Yanci a Musulunci shi ne ‘yancin binciken gaskiya ba guje mata ba.
Kuma ka ce: “Gaskiya daga Ubangijinku take;” to wanda ya ga dama ya yi imani, wanda kuma ya ga dama sai ya kafirta. Lalle kam Mun tanadar wa azzalumai wata wuta wadda katangarta ta kewaye su. Idan kuma suka nemi taimako to za a taimake su ne da ruwa kamar tafasasshen mai da zai riqa toye fuskoki. Tir da wannan abin shan makoma kuma ta munana.” [kahfi: 29]
Ba a siyan imani kuma ba a tilastawa sai an yi shi, sai dai ana zavar sa ne yayin da zuciya ta fahimci kyawun gaskiya.
Sai dai fa samun ‘yanci ba tare da wani nauyi da za a kula da shi ba, yana birkixewa ya zama nadama bayan dama ta kuvuce.
Babu tilastawa a addini, haqiqa shiriya ta riga ta bayyana daban da vata. Don haka duk wanda ya kafirce wa Xagutu, kuma ya yi imani da Allah, to haqiqa ya yi riqo da igiya mafi qarfi wadda ba ta tsinkewa. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. [Baqara: 256]
Faxin Allah: “Babu tilastawa a addini”, ba wai wata alama ba ce kawai, a’a wata haqiqa ce ta Alqur’ani.
Musulunci yana kiranka da ka yi tunani, ba don a tilasta maka ba. Don haka gaskiya a bayyane take ga wanda yake so ya ganta.
Babu tilastawa a addini, haqiqa shiriya ta riga ta bayyana daban da vata. Don haka duk wanda ya kafirce wa Xagutu, kuma ya yi imani da Allah, to haqiqa ya yi riqo da igiya mafi qarfi wadda ba ta tsinkewa. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. [Baqara: 256]
‘Yanci na gaskiya shi ne ka ‘yantu daga bautar mutane da kuma wasu tunane-tunane don ka yi imani da Allah shi kaxai. A yayin da ka kafirce wa xagutu ka yi imani da Allah mahalicci, to a lokacin ne ka yi riqo da igiya mai qarfi.
Ka ce: “Ya ku mutane, haqiqa gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku; duk wanda ya shiriya to ya shiriya ne don kansa; wanda kuma ya vace to lalle ya vace don kansa ne; ni kuwa ba wakili ne a kanku ba.” [Yunus: 108]
Allah ya bijirar da gaskiya ga mutane baki xaya, sannan ya bar wa kowace zuciya ta zavi abin da ya dace da ita. Don haka wanda ya shiryu, to don kansa ya shiryu, wanda kuma ya vata, to sakamakon uqubar vatan na gare shi.

Ba a aiko Annabi don ya tilasta wa wani ba, sai dai an aiko shi ne don ya isar da saqo.
Kuma kowane mutum yana zavar hanyarsa ne da zuciyarsa a gaban Allah. Wannan shi ne ‘yancin da ba ya watsar da imani sai dai ma ya cika shi.
Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya vace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu.” [Nahl: 125]
Alqur’ani ba ya yin kira zuwa ga yin gware tsakanin mutane, sai dai yana yin kira zuwa ga tattaunawa cikin hikima.
Allah ya ce: ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau.”...Wata irin gada ce ta kalmomi masu daxi wadda take gyara abin da tsanantawa take vatawa.
Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya vace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu.” [Nahl: 125]
A Musulunci, tattaunawa ba yaqi ba ne, a’a kira ne ga hankula da kuma zukata da cewa su haxu a bisa hasken gaskiya.
Duk wanda ya yi imani da hikima, to ya yi imani cewa, magana mai daxi tafi kaiwa maqura wurin tasiri sama da amfani da makami.
Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na qut da qut. Ba kowa ake bai wa wannan kyakkyawar xabi’ar ba sai waxanda suka yi haquri, ba kowa ake bai wa ita ba sai mai babban rabo. [Fussilat: 34-35]
Yayin da ka fuskanci munanawa da kyautatawa, to kana karya katangu ne kana kuma gina gadoji.
Alqur’ani yana karantar da mu cewa, su zuciyoyi ana buxe su ne ta hanyar tausasawa ba ta hanyar tursasawa ba.
Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na qut da qut. Ba kowa ake bai wa wannan kyakkyawar xabi’ar ba sai waxanda suka yi haquri, ba kowa ake bai wa ita ba sai mai babban rabo. [Fussilat: 34-35]
Martani mai kyau ba a samunsa sai daga wurin rai mai daraja tare da haquri mai girma. Da irin wannan ladabin ne mutun yake ciruwa daga qiyayya zuwa xan’adamtaka bisa ma’anarta mai faxi.
Yana kuma daga ayoyinsa cewa Ya halitta muku mata daga jinsinku don ku samu nutsuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da jin qai tsakaninku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani. [Rum: 21]
A mahangar Alqur’ani, aure ba abu ne da ake yi don samun abin duniya ba kawai, a’a sai dai shi nitsuwa ce da soyayya da jin qai.
Ayar ba tana magana ne a kan namiji da mace ba kawai, a’a tana magana ne game da zuciyoyi biyu da Allah ya samar da su sashe ga sashe.
Yana kuma daga ayoyinsa cewa Ya halitta muku mata daga jinsinku don ku samu nutsuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da jin qai tsakaninku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani. [Rum: 21]
Yayin da Allah ya sanya soyayya da rahama a tsakanin zukata, to gidaje suna wayar gari sun zama wata ‘yar qaramar Aljanna a gidan duniya.
Soyayya a Musulunci ba abu ne da yake zuwa ya wuce ba, a’a wata mu’ujiza ce daga cikin mu’ujizozin Allah mahalicci.
Ubangijinka kuwa Ya hukunta cewa, kada ku bauta wa (wani) sai Shi kaxai, kuma ku kyautatawa iyaye. Ko dai ya zamanto xayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkansu, to kada ka nuna qosawarka da su, kada kuma ka daka musu tsawa; ka yi musu magana ta girmamawa. Ka kuma qasqantar da kai gare su don tausayawa, ka kuma ce: “Ubangijina Ka ji qan su kamar yadda suka raine ni ina xan qarami.” [Isra: 23-24]
Kafin Alqur’ani ya yi umarni da a yi salla, sai da ya yi wasici da a kyautata wa iyaye.
Kyautata musu ba wai sa ka alheri ba ne da alheri, a’a godiya ce ta rayuwar da ta yi mana baiwar samun komai.
Ubangijinka kuwa Ya hukunta cewa, kada ku bauta wa (wani) sai Shi kaxai, kuma ku kyautatawa iyaye. Ko dai ya zamanto xayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkansu, to kada ka nuna qosawarka da su, kada kuma ka daka musu tsawa; ka yi musu magana ta girmamawa. Ka kuma qasqantar da kai gare su don tausayawa, ka kuma ce: “Ubangijina Ka ji qan su kamar yadda suka raine ni ina xan qarami.” [Isra: 23-24]
Hakanan kuma biyayyar ba ta buqatuwa zuwa ga wasu manyan ayyuka, wani lokaci kalma tattausa ma ta isa ta wadatar.
Alqur’ani ya koyar da mu cewa, hatta da nuna qosawa ma yana cutar da zuciyar mahaifa. Don haka tausayawa ita ce mafi qololuwar godiya a gare su.