Saboda Me Ake Jarabtarmu."

Saboda Me Ake Jarabtarmu."

"Kuma lalle za Mu jarrabe ku”
A haka Allah ya fara magana a ayar.
“Da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta 'ya'yan itatuwa”. [Bakara: 155]
Shin ka yi raki?
Kada ka tsaya yayin da kake jin radadi...
A’a, ka tuna da karshen lamarin.
“Don haka ka yi albishir ga masu hakuri”.
Allah ba ya jarabtarka don ya azabtar da kai...
Sai dai don ya tsarkakeka, ya kuma kusantar da kai gare shi, ya kuma daukaka ka.
“Lalle Allah Yana tare da masu hakuri” [Bakara: 153]
Yayin da bala’i ya tsananta...kada ka gudu.
Ka kusanto zuwa ga wanda yake yaye tsanani.
Ka fadeta kamar yadda Ubangijinka ya umarceka:
“Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare Shi muke komawa.” [Bakara: 156]
Cikin dukkan wani radadi...akwai kira zuwa ga dawowa (ga Allah) ba guje masa ba.
Kai fa kana gaban Masani ne Mai bayar da labarin komai...
Don haka ka dogara a gare shi.
Kuma ka sani cewa ba zai tozarta ka ba.

404
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya