Sannan lokacin da manzanninsu suka zo musu da (ayoyi) bayyanannu.."
Sannan lokacin da manzanninsu suka zo musu da (ayoyi) bayyanannu, sai suka nuna farin ciki da ilimin da ke gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu
To lokacin da suka ga azabarmu sai suka ce: “Mun yi imani da Allah Shi kaxai, mun kuma kafirce wa abin da muka kasance muna yin shirka da shi.”
To imaninsu bai zamanto zai amfane su ba yayin da suka ga azabarmu; wannan sunna ce ta Allah wadda ta shuxe a kan bayinsa. Kafirai kuma sun yi asara a nan
656
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category