Alqur’ani da Tambayar Gaskiyar Lamari."
Akwai wasu lokuta da muke tsayawa a gaban wasu tambayoyi da ba sa qarewa, misali:
Me ya sa Allah ya haliccemu?
Kuma me ya sa muke wucewa ta hanyar wasu tajribobi da suke kawo mana canji a cikin ranmu?
Kuma ta ya ya za mu fahimci gaskiya a tsakiyar duniyar da take cike da mabambantan sautuka da ra’ayoyi da zace-zace?
Alqur’ani ba littafin hukunce-hukunce ba ne ba kaxai, a’a Alqur’ani makaranta ce da take horar da hankali a kan ya riqa duba zuwa ga halitta da ma’aunai mabambanta.
Ma’auni ne da zai koyar da kai yadda za ka yi bincike game da haqiqanin lamari ba tare da tsoro ba. Ma’auni ne da zai koyar da kai yadda za ka bambance tsakanin abin da yake qawalwalniya ce da abin da yake gaskiya.
Allah Ta’ala yana cewa: “Waxanda suke sauraron magana sai su bi mafi kyawunta, waxannan su ne waxanda Allah Ya shiriya, kuma waxannan su ne ma’abota hankula.”. [Zumar: 18]
Wannan ayar ba tana kira ne zuwa ga sauraro ba kawai, a’a tana yin kira ne don yin tunani da bambance tsakanin abubuwa, da kuma neman abin da ya fi kyau.
Kamar tana faxa maka cewa, ka sanya hankalinka ya zama qofa, ba ya zama rufaffen akwatu ba.
Yayin da kake tafiya tare da Alqur’ani, yadda kake kallon abubuwa zai canja a tattare da kai.
Ba za ka riqa ganin bala’i a matsayin zallar cuta ba, ko ka riqa ganin ni’ima a matsayin hutu ba.
Sai dai za ka riqa ganin cewa dukkan wani abu da ke faruwa akwai wata manufa a qarqashin faruwarsa. Kuma Allah Ta’ala yana tarbiyantarka ne ta dalilin mabambantan yanayi da kake wucewa ta cikinsu, kuma a hankali yana yaye maka hikimar da ke cikin hakan, taku bayan taku.
Alqur’ani yana horar da hankali a kan yin haquri da kuma amintuwa da qin bin shubuhohi ko hayaniya.
Hakanan Alqur’ani yana qara tsara maka tunane-tunanenka, ya sa ka riqa kallon halitta kamar yadda Allah yake so a kalleta, wato: a bayyane, kuma a miqe, wadda take cike da manufa da ma’ana.
Yayin da ka sa Alqur’ani a tunaninka, za ka ga gaskiya ba tare da ka sha wahala ba. Kuma za ka ga hanya ba tare da ka ruxe ba, sannan zuciyarka za ta qara samun tabbatuwa sama da yadda kake tsammani.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category