Ya ku waxanda suka yi imani, bayinku da kuma waxanda ba su isa mafarki ba a cikinku (watau waxanda ba su balaga ba) su nemi izininku sau uku. Kafin sallar Asuba da sanda kuke tuve tufafinku a lokacin garjin rana da kuma bayan sallar Lisha. Lokatai ne guda uku na tsiraicinku . Babu laifi a kanku ko a kansu bayansu (waxannan lokatai). Masu shige da fice ne a gare ku sashinku bisa sashi. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi. Allah kuma Masani ne, Mai hikima
Katika masu alaka
Nuna katika