Ya halicci mutum daga busasshen tavo kamar kasko
Nuna katika
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?(Suratuz Zariyat-21)
Sannan idan aka gama salla sai ku bazu a bayan qasa ku kuma nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa don ku rabauta(AL‑JUMU‘AH-10)
Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassavawar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma’abota hankula(ĀLI ‘IMRĀN-190)
Haqiqa kuna da kyakkyawan abin koyi tare da Manzon Allah, ga wanda yake yin kyakkyawan fata game da Allah da ranar lahira, ya kuma ambaci Allah da yawa(Suratul Ahzab-21)
Haqiqa Mun girmama ‘yan’adam, Muka kuma xauke su (kan ababen hawa) na sarari da na ruwa, Muka kuma arzuta su daga tsarkakan (abubuwa) kuma Muka fifita su a kan wasu da yawa daga abin da Muka halitta nesa ba kusa ba
Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka kiyaye dokokin Allah, to zai sanya muku (hanyar) tsira Ya kuma kankare muku munanan ayyukanku kuma Ya gafarta muku. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne(AL‑ANFĀL-29)