Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi; kuma Ya fari halittar mutum daga tavo
Nuna katika
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?
Ya kuma hore muku abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa gaba xayansu daga gare Shi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani
Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka kiyaye dokokin Allah, to zai sanya muku (hanyar) tsira Ya kuma kankare muku munanan ayyukanku kuma Ya gafarta muku. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne(AL‑ANFĀL-29)
Sannan idan aka gama salla sai ku bazu a bayan qasa ku kuma nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa don ku rabauta(AL‑JUMU‘AH-10)
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?(Suratuz Zariyat-21)
Haqiqa kuna da kyakkyawan abin koyi tare da Manzon Allah, ga wanda yake yin kyakkyawan fata game da Allah da ranar lahira, ya kuma ambaci Allah da yawa(Suratul Ahzab-21)