Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi; kuma Ya fari halittar mutum daga tavo(7- AS-SAJDAH)
Nuna katika
Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku Wanda Ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma Ya halicci matarsa daga shi, kuma Ya yaxa maza da mata masu yawa daga gare su. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye (yanke) zumunci. Lalle Allah Mai kula da ku ne
Ya kuma hore muku abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa gaba xayansu daga gare Shi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani
Haqiqa kuna da kyakkyawan abin koyi tare da Manzon Allah, ga wanda yake yin kyakkyawan fata game da Allah da ranar lahira, ya kuma ambaci Allah da yawa(Suratul Ahzab-21)
Haqiqa Mun girmama ‘yan’adam, Muka kuma xauke su (kan ababen hawa) na sarari da na ruwa, Muka kuma arzuta su daga tsarkakan (abubuwa) kuma Muka fifita su a kan wasu da yawa daga abin da Muka halitta nesa ba kusa ba
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?(Suratuz Zariyat-21)
Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka kiyaye dokokin Allah, to zai sanya muku (hanyar) tsira Ya kuma kankare muku munanan ayyukanku kuma Ya gafarta muku. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne(AL‑ANFĀL-29)