Kowace irin jarumta tana da qarshe. Hakanan ita ma rayuwa tana da qarshe.
Nuna katika
Bayan an gama hayaniyar...to mutum zai zamana shi kaxai daga shi sai zuciyarsa. To a nan ne tambayoyi na gaskiya suke farawa. #Hasken_Alqur’ani#Bayan_wasa#Gaskiya#Hasken_Alqur’ani#Nutsuwar_Zuciya
Mutane suna neman samun farin ciki ta hanyar samun nasarori a gasa...sai dai kuma wasu zukatan suna ci gaba da kasancewa a cikin damuwa ko da kuwa sun samu nasarar. Saboda samun nutsuwa ba shi ne kofin da ake xagawa ba, a’a nutsuwa wani aminci ne na musamman da ake ji a rai.
A cikin kowace gasa ana shan wahala kafin a kai qarshe, haka ma al’amarin yake game da rayuwa. Ita kuma zuciya tana neman abin da zai ba ta nutsuwa ta haqiqa ne. #Hasken_Alqur’ani#Zaman_lafiya#Qwallon_qafa#Ayar_Alqur’ani#Nutsuwar_Zuciya
“Lalle tsanani yana tare da sauqi” [Sharh: 6]
Mutum ya fi qarfin a wulaqanta shi saboda jinsin da ya fito ko launinsa ko garin da ya fito. Darajarsa ta haqiqa ta fi dukkan wani rabe-rabe da za a yi. #Hasken_Alqur’ani#Mutunci_xan’adam#Kofin_duniya#Saqon_Musulunci#Xan’adamtaka
Musulunci ba ya buqatar ka ka zamo cikakke ba tare da rauni ba, sai dai yana buqatar ka da ka san wurin wa za ka koma yayin da ka samu rauni. #Hasken_Alqur’ani#Xabi’ar_dan’adam#Musulunci#Magoya bayan_Qwallon_qafa#Baiwar_Alqur’ani