Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu qauna
Nuna katika
Shiriya tana farawa lokacin da zuciya ta fuskanto wa shiriya da gaskiya, ba lokacin da aka gama fahimta ba. #Shiriya
Ya ku waxanda aka bai wa Littafi, haqiqa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke voyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haqiqa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawaDa shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga du...
Yayin da zuciya ta cika da son Allah, dukkan wasu abubuwa da ake so za su zama ba wani abu ba, kuma ma’auni zai daidaita. #Son_Allah
Alqur’ani ba rubutu ne da ake karantawa ba kawai, sai dai shi wa’azi ne da yake faxakarwa, da kuma waraka da take gyara abu, da rahama da take riqe zuciyarka cikin tausasawa. #Hasken_Alqur’ani
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulm
ALIF LAM RA . Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya