Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu qauna
Nuna katika
Ba daga cikin duhu xaya Alqur’ani yake fitar da kai ba, yana fitar da kai daga cikin duffai masu yawa, zuwa ga haske guda xaya kuma bayyananne. Daga_Duffai_Zuwa_Haske
Abin da ake nufi da ka zavi Allah shi ne, ka ‘yantu daga dukkan wani wanda ba shi ba. #Tauhidi
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri)Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjadaSuka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai
Babu wata buqata da zuciya take da ita face Alqur’ani ya yi bayani game da ita ko kuma ya ba da wata shiriya ko ya kawo rahama game da ita. #Shiriya_Da Rahama.
Alqur’ani ba shiryayyiyar amsa ba ce ba kawai, sai dai haske ne da yake abokantakarka, lokacin da kake can kana laluben wani abu. #Hasken_Shiriya
Son Allah ba da’awa ba ce, sai dai zavi ne da yake canja abubuwan da aka fifita ya ‘yantar da zuciya daga rataya kanta da abin da yake ba na gaskiya ba. #Zuciya_Da Imani