Manufar halittarmu shi ne tsantsanta bauta ga Allah, ba mu tara arziqi ko abinci ba.
#Manufar_Ruhi
Nuna katika
Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al’amarinsa ne. Haqiqa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu
Shin ba za su yi zuzzurfan tunani game da (ayoyin) Alqur’ani ba ne? Kuma da a ce ya kasance daga wajen wani yake ba Allah ba, tabbas da sun sami savani mai yawa a cikin
Shiriya ba ta wanda yake yawan saurare ba ce, a’a shiriya ta wanda yake iya bambance alheri ne, ya kuma yi riqo da mafi kyawunsa. Irin waxannan su ne waxanda Allah ya ba su hankali tsaftatacce da basirar da ba ta kauce wa hanyar gaskiya. #Tsaftatacciyar_Basira
Ba a halicci mutum ba ba tare da manufa ba, tafiyarmu tana farawa ne daga qaramin xigon maniyyi, sannan mu wayi gari mun zama cikakkiyar halitta. Duk da wannan ta ya ya rayuwarmu za ta zamo babu manufa a cikin halittarta. #Ka yi tunani
Yanzu mutum yana tsammanin za a bar shi haka sasaka ?Shin bai kasance wani xigo na maniyyi da ake zuba shi (a mahaifa) ba?Sannan ya zama gudan jini sannan (Allah) Ya halicce (shi) sai Ya daidaita (shi)?
Gaskiya ba ta buqatar ado, ya isheka kawai ka yi tunani game da ita domin gane mavuvvugarta daga Allah take. Ba za a tava samun littafin da babu savani a cikinsa ba, sai dai idan daga Allah yake. #Hasken_Alqur’ani