Manufar halittarmu shi ne tsantsanta bauta ga Allah, ba mu tara arziqi ko abinci ba.
#Manufar_Ruhi
Nuna katika
Yanzu mutum yana tsammanin za a bar shi haka sasaka ?Shin bai kasance wani xigo na maniyyi da ake zuba shi (a mahaifa) ba?Sannan ya zama gudan jini sannan (Allah) Ya halicce (shi) sai Ya daidaita (shi)?
Ya isheka ka yi duba zuwa halittar sammai don ka ga irin tsarin da aka xorasu a kai wanda babu wata tawaya da ta haxu dashi. Halitta ce da aka kyautata, tana yi maka raxa da cewa, Hannun Allah Mai rahama, babu tawaya a tattare da shi. #Ayoyin_Sammai
Arziqi yana zuwa ta inda mutum ba ya tsammani. Don haka idan ka dogara ga Allah da gaske, to Allah zai isar maka, ya ba ka sama da abin da kake fatan ka samu. #Ka Aminta_Da Allah
A yayin da mutum ya tsarkake zuciyarsa daga dukkan abin da zai iya vatar dashi, ya koma zuwa ga Allah komawa ta gaskiya, to Allah zai buxe masa qofa, ya kuma lulluve shi da bushara, ya kuma ja shi zuwa ga mafi tsaftar hanyar gaskiya. #Shiriyar_Haske
Shiriya ba ta wanda yake yawan saurare ba ce, a’a shiriya ta wanda yake iya bambance alheri ne, ya kuma yi riqo da mafi kyawunsa. Irin waxannan su ne waxanda Allah ya ba su hankali tsaftatacce da basirar da ba ta kauce wa hanyar gaskiya. #Tsaftatacciyar_Basira
Duk wanda ya miqa lamarinsa ga Allah, to zai ga qofofin alheri suna ta buxe masa ba tare da wani sababi na zahiri ba. Kowane abu yana wurin Allah da ma’auni kyautatacce da iyakar da ba za ta sauya ba. #Arziqi_Da Qaddara.