(Allah) Mai rahama.
Shi Ya koyar da Alqur’ani.
Ya halicci mutum .
Ya koyar da shi bayani.
Nuna katika
Littafi ne mai albarka da Muka saukar maka da shi domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa, don kuma masu hankula su wa’azantu
Nawa nawa ne daga cikin zukata wadanda suka nesanta daga ambaton Allah ta’ala, har ya zamana sun yi sakayau sun kekashe. Amma kiran Allah Ubangiji bai gushe ba yana kwankwasa kofar kira zuwa ga a dawo... Shin lokacin da za su yi taushin ya yi? Fadakuwar_Zukata.
(Su ne) waxanda idan wata musiba ta same su sai su ce: “Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare Shi muke komawa.”
Gafala tana kekasar da zukata Ambaton Allah kuma yana tausasata ya kuma sa ta yin sabuwar rayuwa. Kada ka bari duniya ta tafiyar da kai_ka dawo yanzu-yanzu. Komawa_Zuwa ga_Allah
Ba a yawaita magana yayin da ake cikin musiba, Ya isheka ka yi ta nanata fadin: “mu na Allah ne, kuma zuwa gare shi za mu koma” a cikin ranka. Domin a cikin fadar hakan akwai, mika wuya da yarda da kuma nutsuwa. #Mika wuya_da komawa.
Alkur’ani ba littafi ne da ake karantawa ba kawai, A’a, an saukar dashi ne don a yi tuntuntuni game dashi...don haka duk wanda bai yi tuntuntunin ma’anoninsa ba, to kamar akwai wani rufi a kan zuciyarsa wanda ba za a iya bude shi ba. Tuntunin_Alkur’ani