(Allah) Mai rahama.
Shi Ya koyar da Alqur’ani.
Ya halicci mutum .
Ya koyar da shi bayani.
Nuna katika
Alkur’ani ba littafi ne da ake karantawa ba kawai, A’a, an saukar dashi ne don a yi tuntuntuni game dashi...don haka duk wanda bai yi tuntuntunin ma’anoninsa ba, to kamar akwai wani rufi a kan zuciyarsa wanda ba za a iya bude shi ba. Tuntunin_Alkur’ani
Alkur’ani yana shiryar da kai zuwa hanya mafi mikewa, Ba wai ta hanyar umarni da hani ba kawai, a’a a dukkan tsarin rayuwarka yana yi maka jagora zuwa ga rabauta da dacewa. Alkur’ani_Jagoran_Rayuwa#
Ya ku waxanda suka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haquri da salla. Lalle Allah Yana tare da masu haquri
Alkur’ani ya kasance shi ne ni’imar farko bayan rahama, Kuma ya zama kamar mafi girman abin da za a koyar da mutum bayan an halicce shi...shi ne maganar Allah. #Alkur’ani_Rahama
Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa
Jarabawoyi da Allah yake yi wa bayi, ba dalili ne da yake nuna fushin Ubangiji ba, a’a wata dama ce da masu hakuri suke samu don su daukaka. Tsoro da yunwa da rashi....dukkansu darussa ne na kara samun yarda da Allah. #Jarabta_da hakuri.