Sannan bayansu Muka mayar da ku madadinsu a bayan qasa don Mu ga me za ku aikata
Nuna katika
Kada ka wuce iyaka a cikin aikinka, lalle Allah ya ganin abin da kake aikatawa. Ka tsayu a kan abin da aka umarceka, da sannu za ka samu tsira a duniya da lahira. Tuba_Tsayuwa a kan tafarki madaidaici
Amana nauyi ne mai girma da Allah ya bijirar dashi ga manyan halittu, amma suka ki yarda su karba, amma dan’adam yayi jara’a ya dauketa! Shin mun san kuwa hakikanin amanar da muka dauka a wuyayanmu? #Amana#
Ba a bayar da Aljannar Firdaus sai ga wanda yayi imani yayi ayyuka nagari. Sakamako ne wanda ba za a iya kwatanta shi da dukiya ko matsayi ba. Lalle ita (Firdausi) Aljanna ce ta dawwama ga wanda ya kasance a kan tafarki ingantacce. #Aljannar_Firdaus
Dukkan aiki nagari wanda zai kusantar da kai zuwa Aljannar Firdausi koda taqi daya ne, ta yadda ba za a musanyata ba ko a a juyar da kai ga barinta, to wannan ni’ima ce ta har abada. Lalle ita ce rayuwa ta hakika wadda bata buqatar musaye. #Dawwama_a_Aljanna
Lalle Allah Yana umartar ku da ku mayar da amanoni ga masu su, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, to ku yi hukunci da adalci. Lalle kam madalla da abin da Allah Yake muku wa’azi da shi. Lalle Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani
Tsayuwa a kan imani yana baka aminci a zuciyarka da aminci a lahira, da kuma Aljannar da za a cika maka dukkan burikanka a lahira. Ka tuna; mala’iku fa na tare da kai a kowane lokaci. #Tsayuwa a kan_Imani