Haqiqa wanda ya tsarkake shi (ran) ya rabauta
Haqiqa kuma wanda ya binne shi da savo ya tave
Nuna katika
Mutuwa gaskiya ce, kuma haduwa ce da Allah. Ka yi aiki don duniyarka kamar za ka rayu har abada, kuma don lahirarka kamar za ka mutu gobe.#Tunanin_Mutuwa #Lahira
Allah yana umarni da adalci a duk al'amura. Kada ka bar rashin adalci ya dagula rayuwarka ko ta wasu. #Adalci_Ginshikin_Rayuwa #Tsoron_Allah
(Ka tuna) ranar da za ka ga muminai maza da muminai mata haskensu yana tafiya ta gabansu da ta damansu, (ana cewa da su): “Albishirinku a wannan rana (su ne) gidajen Aljanna da qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma.”A ranar da munafukai maza da munafukai mata za su riqa cewa da waxanda suka yi...
Komai dabarar shaidan, tana da rauni a gaban wanda ya nemi taimakon Allah. Kada ka ji tsoro, ka kasance tare da Allah koyaushe. #Dabarar_Shaitan #Dawwamani
Haqiqa kuma Mun halicci mutum, kuma Mun san abin da ransa yake saqa masa; kuma Mu Muka fi kusa da shi fiye da jijiyar wuyansa
Ya ku waxanda suka yi imani, ku zamo masu tsayawa qyam da haqqoqin Allah, kuna masu yin shaida da adalci; kuma kada qin waxansu mutane ya hana ku yi musu adalci. Ku yi adalci shi ne mafi kusanci ga taqawa. Kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne