Haquri mai kyau

Haquri mai kyau


A yayin da ake cikin ruxanin rayuwa da jujjuyawarta, haquri yana kasancewa kamar haske da zai haskaka hanya mai duhu, kamar yadda Allah Ta’ala ya faxa a cikin Suratul Ma’arij: “Ka yi haquri, haquri mai kyau”.

 

Haquri mai kyau shi ne haqurin da babu raki a cikinsa, haqurin da yake xaukaka ran mai shi sama da raxaxin da take ji, ya gina mata wasu gadoji na fata a saman kogunan xebe qauna. Irin wannan haqurin ba jira ne marar kyau ba, a’a haquri ne na aiki da imani da kuma fatan cewa lokacin yaye damuwa a kusa yake.

 

A yayin da ake tafiya a zangon rayuwa, haquri yana zama wani mabuxi da ake cin galaba a kan qalubale da tsananin da ake fuskanta.

“Ka yi  haquri haquri mai kyau”. Suratul Ma’arij, Aya ta 5.

 

Kalmomi ne da suke vuvvugowa daga hikimar Ubangiji a cikin Suratul Ma’arij, waxanda suke kiranmu zuwa ga yin haqurin da ba a cakuxa shi da raki ba.

 

Haquri mai kyau shi ne haqurin da ya siffantu da yarda da kuma kyakkyawan fata, ta yadda mai haquri zai kalli sama yana mai imani cewa, kowane baqin girgije, to qarqashinsa akwai rana mai haske.

 

Kuma kamar yadda Allah ya yi alqawari a cikin Suratuz Zumar inda yake cewa, “Kaxai ana cika wa masu haquri ladansu ba tare da lissafi ba”. Don haka lallai ladan da yake jiran masu haquri ba shi da iyaka, ya wuce duk wani tunani, da kuma kishiyantar girman sakamakon da za a samu daga Allah Ta’ala

76 35

kundina masu alaka

Bude kundin Islama

Kundi

Yi tarayya