Alƙur'ani Shi Ne Hanyar Haɓaka
See other videos from same category
Dan Adam A Cikin Alƙur'an
Allah Yana nufin yi muku bayani ne, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suka gabace ku, kuma Ya karvi tubanku. Kuma Allah Mai yawan sani ne, Mai hikimaKuma Allah Yana nufin Ya karvi tubanku ne, amma waxanda suke bin sha’awace-sha’awace, su kuma suna nufin ku karkace karkacewa mai girma
Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima
Bukatuwar Mutane Zuwa Ga Wahayin Ubangiji
Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa
Sannan lokacin da manzanninsu suka zo musu da (ayoyi) bayyanannu, sai suka nuna farin ciki da ilimin da ke gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu To lokacin da suka ga azabarmu sai suka ce: “Mun yi imani da Allah Shi kaxai, mun kuma kafirce wa abin da muka kasance muna yin shirka da shi.” To imaninsu bai zamanto zai a...