Dan Adam A Cikin Alƙur'an
See other videos from same category
To idan ba su amsa maka ba, to ka sani cewa ba abin da suke bi sai soye-soyen zukatansu kawai. Ba kuwa wanda ya fi vacewa kamar wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
Allah Yana nufin yi muku bayani ne, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suka gabace ku, kuma Ya karvi tubanku. Kuma Allah Mai yawan sani ne, Mai hikimaKuma Allah Yana nufin Ya karvi tubanku ne, amma waxanda suke bin sha’awace-sha’awace, su kuma suna nufin ku karkace karkacewa mai girma
Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa
Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima
Alƙur'ani Shi Ne Hanyar Haɓaka
Bukatuwar Mutane Zuwa Ga Wahayin Ubangiji