Ka yi Tunani Game da Halittar Duniya Qofa ce Ta Yin Imani."

Ka yi Tunani Game da Halittar Duniya Qofa ce Ta Yin Imani."

Ka sa a ranka cewa kana yin duba zuwa sama a cikin daren da babu hayaniya a cikinsa.
Ba ka tunanin sunayen taurari ko ma’aunan ilimin kimiyar Physics.
Kawai ka kalli sama, ka bar zuciyarka ta yi tambaya kafin hankalinka ya yi ta shi tambayar: Ta ya ya aka samu irin wannan sama mai ban-qaye haxe da qwarewa, ba tare da samun wanda ya samar da ita ba?
Alqur’ani yana komar da hankali zuwa ga wannan tunanin ta sauqaqqiyar hanya kuma mai zurfi, inda Allah ya ce: “Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassavawar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma’abota hankula.” [Ali Imran: 190]
Kamar ayar tana faxa maka cewa: Duniya ba abar kallo ba ce ba kawai, a’a wani saqo ne ake isar maka. Kuma kowane yanki na ta wata hujja ce, sai dai kuma hujja ce wadda ba wanda zai iya fahimtarta sai wanda ya yi tunani da zuciyarsa da hankalinsa a tare.
Ba a halicci duniya don rayuwarka ba kawai, duniya wani littafi ne da aka buxe, shafukanta su ne taurari, saxarorinta kuma su ne duwatsu, abubuwan da suke rarrabeta su ne juyawar zamani.
A yayin da za ka fara karatu game da duniya, za ka gane cewa, imani ba wani labari ba ne da aka wajabta maka shi, sai dai shi sakamako ne na yanayin xabi’ar tuntuntuni na gaskiya.
Ba ka buqatar ka zama malamin taurari kafin ka fahimta, ko kuma masanin falsafa don ka yi tambaya.
Ya isheka ka tsaya ka kalli sama kawai. Ka bar tambayarka ta yi kai-kawo a cikin ranka, wato: Ta ya ya aka ajiye komai a bigirensa? Kuma saboda me muke jin cewa, akwai wani abu mafi girma da muke son gani yake ta maimaituwa a cikin ranmu?
Duniya ba ta yin ihu, sai dai tana yin tafiya. Kuma tafiyar duniya ita ce hanya. Duk wanda ya bi ta da gaskiya, to Allah zai buxe masa wata qofa ta haske wadda ba za a tava rufeta ba.

50
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya