Fifiko Tsakanin Mutane
A wannan duniyar...(mutane) suna daukaka sha’anin mutum saboda dukiyarsa.
Su kuma tsarkake wani saboda zubinsa da launinsa.
Suna kuma nisantar wanda ba ya mallakar komai.
Sai dai Alkur’ani yana rusa wannan wahamin....yana gina ka’idar da ta saba masa: “Ya ku mutane, lalle Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, Muka kuma sanya ku al’ummu da qabilu don ku san juna. Lalle mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku taqawa. Lalle Allah Masanin sarari ne, Masanin voye. [Hujurat: 13]
Girmanka ba a asusun bankinka yake ba.
Sannan ba a shuhurarka yake ba...ko a sunan danginka ba
Girmanka a wurin Allah shi ne ka samu takawa.
Takawar da take haifar gaskiya...adalci...da rahama
Me kake zato da a ce dukkan mutane an san su ta dalilin wannan ma’aunin...
Ya zamana zaman duniya na gudana ba tare da nuna bambancin launin fata ba...ba tare da nuna dagawa ba...ba tare da girman kai ba.
Wannan shi ne kira...ba kira irin na ‘yan duniya ba...a’a kira mai tasiri daga sama.
Cewa ka zamo mutum...kafin ka zamo wani abu na daban.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category