Sukar Darwin Theory Hu
See other videos from same category
Kuma daga Alqur’ani Muna saukar da abin da yake shi waraka ne da kuma rahama ga muminai; ba kuma zai qari azzalumai (da komai) ba sai tavewa
Sulhu Tsakanin Mutane
Kuma kada ku bai wa (marayu) wawaye dukiyoyinku wadda Allah Ya sanya rayuwarku take tsaye a kai, kuma ku ciyar da su, kuma ku tufatar da su daga cikinta, kuma ku faxa musu magana mai daxi
Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci mutum daga busasshen tavo mai amo na wani yumvu mai wari
Ya kuma hore muku abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa gaba xayansu daga gare Shi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani
Yanzu waxanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da qasa a haxe suke, sannan Muka raba su[1]; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?