Yanci Na Haqiqa A Cikin Alqur’ani

Yanci Na Haqiqa A Cikin Alqur’ani

Ba a siyan ‘yanci
Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa”. [Jasiya: 23]
Shin kana tunanin kai ‘yantacce ne?
Yayin da za ka yi fushi ka yi ihu, kuma yayin da ka za ka yi sha’awar wani abu ka yi rauni, yayin da mutane za su yabe ka xaukaka, da kuma yayin da za su zargeka....???
Ina ‘yanci a cikin hakan?

Alqur’ani ba da jiki yake magana ba kawai, a’a har ruhi ma yana magana dashi.
Yana magana da kai cikin tausasawa mai ban mamaki: ka ‘yantar da kanka kafin ka ‘yantar da wani.
Ka ‘yantu daga tsoron da zai hanaka faxar gaskiya
Ka ‘yantu daga kwaxayin da zai tafiyar maka da daidaitonka.
Ka ‘yantu daga al’adar da za ta bice maka haskenka a ko da yaushe alhali kuma kana murmushi.
Bautar Allah ba dabaibayi ba ce, sai dai ita ‘yanci ce.
Yayin da ka yi sujjada ba halaka ka yi ba, a’a waraka ma kake samu
Yayin da ka qasqantar wa da Allah kai, to ba za ka wulaqanta ba, sai dai ma xaukaka da za ka samu.
‘Yanci na gaskiya ba shi ne ka aikata abin da ka ga dama ba, a’a ‘yanci na gaskiya shi ne ka zavi abin da zai yardar da wanda ya halicceka.
Duk lokacin da ka kusanci Allah, to a lokacin ne ka nisanci dukkan wani dabaibayin wani ba kai ba.
Wannan shi ne ‘yancin da ba a siya da kuxi kuma mulki ba ya bayar da shi, shi irinsa kyautar ake yi da wanda ya furta “la ilaha illallah’ daga qoqon zuciyarsa, tare da sanin ma’anarta.

112
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya