Al Qur'ani Da Ci Gaban Al Ummah
See other videos from same category
Ya kai wannan Annabi, faxa wa matanka da ‘ya’yanka mata da kuma matan muminai (cewa) su sanya lulluvinsu. Wannan shi ya fi sanya wa a gane su, don kada a cuce su. Allah kuma Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama
Bambanci Tsakanin Maganin Al Qur'ani Da Maganin Yammacin Don Matsalolin Al'umma
Bukatar Wahayi
Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma
Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima
Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya haxa tsakanin zukatanku, sai kuka zamo ‘yan’uwan juna a sakamakon ni’imarsa, a da kuma kun kasance a kan gavar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyin...