Dan Adam A Cikin Alƙur'an
See other videos from same category
Kuma ka tuna sa’adda Ubangijinka Ya ce da mala’iku: “Lalle ni zan sanya wani halifa[1] a bayan qasa.” Suka ce: “Yanzu za Ka sanya mata wanda zai yi varna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali ga mu muna tasbihi tare da gode Maka, kuma muna tsarkake Ka?” (Allah) Ya ce: “Ni fa tabbas Na san abin da ku ba ku sani ba.”
Yanzu mutum ba ya gani cewa Mu Muka halicce shi daga maniyyi, sai ga shi ya zama mai jayayya a fili?Ya kuma buga mana misali, kuma ya manta da halittarsa (yayin da) ya ce: “Wane ne zai raya qasusuwa, alhali kuma sun rududduge?Ka ce: “Wannan da Ya fare su tun farko Shi ne zai raya su; Shi kuwa Masanin kowacce irin halitta ne
Alƙur'ani Shi Ne Hanyar Haɓaka
Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassavawar dare da rana da jiragen ruwa da suke tafiya a kan ruwa da abin da yake amfanar mutane da kuma abin da Allah Ya saukar daga sama na ruwa, Ya rayar da qasa da shi bayan mutuwarta, Ya kuma yaxa duk wata halitta mai tafiya a cikin (qasa) da jujjuyawar iska, da kuma girgije da aka hore shi tsakanin sam...
Bukatuwar Mutane Zuwa Ga Wahayin Ubangiji
Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima