Sadaka da Karamci."

Sadaka da Karamci."

A cikin kowane birni akwai mutumin da yake dakon hannun da zai miqo masa wani abu. Zai iya kasancewa wata uwa ne da ba za ta iya magana ba take kuka game da yunwar da yaranta suke ciki. Ko kuma ya kasance xan yaro ne da yake yin murmushi duk da cewa yana cikin wahala. Ko kuma ya kasance mutum ne ya kwanta yana bacci amma kuma zuciyarsa a cike take da damuwa.
Karamci ba shi ne bayar da dukiya ba kawai, a’a karamci shi ne a samu zuciya mai kwararar da jin qai, da daddaxar magana da murmushi ko kuma sumbantar goshin qaramin yaro. Wannan ita ce sadaka ta haqiqa.
Allah Ta’ala yana cewa: “Misalin waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, kamar misalin qwaya xaya ce da ta fitar da zangarniya bakwai, a cikinta kowace zangarniya kuma (aka sami) qwaya xari. Kuma Allah Yana ninninkawa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.” [Baqars: 261]
Sadaka ba asara ba ce, a’a ita dalili ce ta samun qaruwa a rayuwa. Tana haskaka rayuwar wasu, sannan kuma tana sauqaqa nauyin da yake kan wasu rayukan.
Duk sanda aka baka wani abu, sai ka ji zuciyarka ta yi sakayau, sai ka ji kamar ranka ya tashi ya yi tsuntsu zuwa sama.
Ka yi tunanin wata kyauta ko sadaka da aka yi maka ba tare da kana dakon zuwanta ba.
Murmushi yana dasa kyakkyawan fata a rai. Hakanan ita ma zuciya mai vuvvugar da rahama da tausayi. Waxannan abubuwa su ne sadakoki mafi girma."

41
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya