Kada Ka Kauracewa Alqur’ani
Allah Ta’ala yace: “Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa.” [Furqan: 30]
Daga cikin ayoyi da suka fi radadi...
Annabi (S.A.W) ya kai kukanmu zuwa ga Ubangijinsa.
Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa.”
Bai ce sun kafirce masa ba... a’a sun kaurace masa.
Kana karanta shi? E.
Sai dai yaushe rabon da ka yi kuka saboda ka karanta wata aya?
Ko kuma ka yi sujjada don godiya saboda karanta wani alkawari?
Ko kuma zuciyarka ta girgiza saboda karanta wani gargadi?
Kaurace wa Alqur’ani bai takaita a kan barin Mus’hafi a kan Kanta ba...
A’a ya hada da ka fitar da shi daga cikin rayuwarka
Ka koma zuwa gare shi...koda ta hanyar karanta aya daya ne a kullum.
Aya daya ....da sautinka, da zuciyarka, kana halarce.
Alqur’ani ba ya juyar da wanda ya fuskanto shi
Ba ya kwankwasa zuciya face ya bar wani tasiri a cikinta.
Kada ka zamo cikin wadanda aka kai kukansu..
A’a ka ka zamo cikin wadanda suka dawo
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category