Shin Kana Neman Haske?
Allah Ta’ala yana cewa: Allah Shi ne Majivincin lamarin waxanda suka yi imani, Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske; [Baqara: 257]
Shin wani lokaci kana jin cewa kana cikin dimuwa....
Ba ka san me yasa kake rayuwa ba, kuma ba ka san ina kake nufa ba?
Dukkan hanyoyi a cushe suke..
Kuma dukkan sautuka suna shiga cikin juna
Amma kai kuma neman haske kawai kake...
Hasken da ba ya bicewa..
Hasken da ba ya canjawa saboda cakuduwar mutane ko yanayi
Alqur’ani ba nassi ne na addini ba kawai..
Shi haske ne a karan-kansa.
Allah Ta’ala yana cewa: Allah Shi ne Majivincin lamarin waxanda suka yi imani, Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske;
Yayin da ka karanta Alkur’ani a karon fari...
Za ka ji kamar wani ne yake shafaka da hannunka ta ciki
Yana shiryar da kai, yana sa maka nutsuwa, yana ratsa zuciyarka...
Kawai ka karanta shi.. ka karanta shi.
Da sannu za ka san a ina hasken yake.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category