Tattaunawa A cikin Alqur’ani

Tattaunawa A cikin Alqur’ani

Yayin da Alqur’ani yake koyar damu yadda za mu kasance yayin da aka samu savani.
Allah yana cewa: “kuma ku faxa musu magana mai daxi.”. Nisa’i: 5
Bai umarcemu da mu yi galaba ba yayin jayayya, ko kuma mu rufe bakin wanda aka samu savani dashi, sai dai mu samu fahimtar juna ta hanyar tattaunawa.

Alqur’ani ya koyar damu cewa, magana ba makami ba ce, a’a magana amina ce.
Don haka xaga murya ba ya nufin qarfi, kuma wani lokaci ma yin shiru ya fi kai wa maqura sama da a kawo dalili dubu.
Allah Ta’ala yana cewa: “kuma ku faxa musu magana mai daxi.”
Kalma ce guda xaya: Magana mai daxi. Amma kuma ta qunshi ladabi da rahama da girmamawa ga wanda ba ya fahimtarka ko wanda bai yarda da kai ba.
A cikin Alqur’ani, tattaunawa ba ta nufin sauka daga kan matsaya, kuma ba qalubale ba ce, sai dai ita gina wata gada ce daga abin da aka fahimta, wato shi ne ka saurara don ka fahimta ba don ka mayar da martani ba.
A yayin da ka samu savani da wani, ka tuna cewa ba manufar ita ce ka kayar da shi ba, a’a manufar ita ce ka sadar da haske zuwa gare shi.
Wannan shi ne yaren Alqur’ani:
Yana yin jayayya da abin da ya fi kyawu, har da waxanda suke adawa dashi
Saboda ita magana idan ta fito da tsaftatacciyar zuciya, to za ta isa zuwa ga zuciyar da take neman gaskiya ko da bayan wani lokaci ne

97
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya