Ashe Har Yanzu Lokaci Bai Yi Ba

Ashe Har Yanzu Lokaci Bai Yi Ba

Yanzu lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani zukatansu su yi taushi da zikirin Allah da kuma abin da Ya saukar na gaskiya.” [Suratul Hadid: 16]
Muna sauraron Alkur’ani....
Sai dai kuma kamar muna sauraronsa ne bisa al’ada, ba a matsayin sako ba.
Shin ka taba gwada sauraro da zuciyarka ba da kunnuwanka ba?
Ka kula....
Kai fa kana sauraron maganar Allah ne...
Allah wanda ya halicceka ya surantaka ya kuma daidaitaka.
“Littafi ne mai albarka da Muka saukar maka da shi domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa”. [Sad: 29]
Kowace aya kira ne, kuma kowace kalma wata dama ce....
“Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi.” [Ankabut: 45]
Shin ka fahimta?
Shin lokacin da za ka yi salla ta gaskiya ya yi?
Shi ne cewa ka saurari ayoyi kamar don kai kadai aka saukar dasu?
Dukkan wani kira a cikin Alkur’ani na:
“Ya ku wadanda suka yi imani”.
Kira ne zuwa gareka...kai a karan-kanka
Don haka ka yi shiru ka ba da aron kunnuwanka...kuma amsa kiran.
Ka dawo yanzu-yanzu...kiran ba ya yin jira.

404
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya