Ya ku mutane, idan kun zamanto cikin kokwanton tashi (bayan mutuwa), to lalle Mu Muka halicce ku daga qasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba, don Mu bayyana muku (Ikonmu). Kuma Muna tabbatar da abin da Muka ga dama a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci qayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikar qarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karvi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi qasqantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani. Za ka kuma ga qasa a qeqashe, sannan idan Muka saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura kuma ta fitar da kowanne irin tsiro mai qayatarwa.”. [Hajj: 5]
Katika masu alaka
Nuna katika