Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa’azi ga masu taqawa
Nuna katika
Allah Shi ne Majivincin lamarin waxanda suka yi imani, Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske; waxanda suka kafirce kuwa, majivinta lamarinsu su ne xagutai, suna fitar da su daga haske zuwa duffai. Waxannan su ne ‘yan wuta; su masu dawwama ne a cikinta
A’a bayani ne da shiriya ga wanda zuciyarsa ta rayu don gaskiya. #Muryar_Gaskiya
Ayoyi ba haruffa ne da ake haddacewa ba kawai... A’a sakonni ne daga sama...da ake fahimta suke kuma kawo canji #Rayuwa_tare da_aya
Kauracewa ba ta nufin mantawa kawai... A’a tana nufin mu rayu amma kamar Alqur’ani bai damemu ba. #Kada_Kaurace masa
Alqur’ani ba ya kwankwasa kunnenka....sai dai zuciyarka, don haka idan ka budeta za ta ji abin da ba ta ji ba a baya. #ka saurari_Alqur’ani
Ba sharadi ba ne sai ka fahimci komai. Ya isheka kawai ka bude zuciyarka...Allah ya sawwake littafinsa ga wanda ya ga dama. #Haske_Ga wanda_Ya neme shi