Lalle masu haquri ne kawai ake cika wa ladansu ba da lissafi ba.”
Browse Islamic cards
Rayuwa ba ta rabuwa da jarrabawoyi da ibtila’oi, sai dai haquri yakan bamu qarfin da za mu fuskance su ta hanyar tabbatuwa da kyakkyawan fata. Haquri yayin fuskantar tsanani yana bukatar qarfin imani da qaqqarfan qudiri ba sakwa-sakwa ba. Don haka yayin da za mu yi haquri za mu tsinci kanmu muna qaruwa da ci gaba ta hanyoyin da ba mu tava tsammani...
lalle wanda ya kiyaye dokokin (Allah) ya kuma yi haquri, to tabbas Allah ba Ya tozarta sakamakon masu kyautatawa.”
Dukkan wata manufa da take da muhimmanci ana buqatar haquri da dagewa don a cimmata, wannan ya haxa da abin da yake da alaqa da yin zarra a sha’anin karatu, ko gina wani babban aiki ake so ya yi nasara, ko abin da ya shafi bunqasa kai, to lalle ana xaukar haquri a matsayin abokin tafiya a irin wannan tafiyar yayin da muke fuskantar rashin cin nasar...
A yayin da ake cikin ruxanin rayuwa da jujjuyawarta, haquri yana kasancewa kamar haske da zai haskaka hanya mai duhu, kamar yadda Allah Ta’ala ya faxa a cikin Suratul Ma’arij: “Ka yi haquri, haquri mai kyau”. Haquri mai kyau shi ne haqurin da babu raki a cikinsa, haqurin da yake xaukaka ran mai shi sama da raxaxin da take ji, ya gina mata...
Kuma ka yi haquri da hukuncin Ubangijika, don ko lalle kana qarqashin lurarmu; kuma ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka lokacin da za ka tashi (daga bacci)
Yin haquri bai taqaita a kan juriya yayin tsanani ba kawai, a’a ya haxa da yin ado da qawa da kyawawan xabi’u waxanda ake yaba yayin mu’amalantar sauran mutane. Yin haquri a bisa cutarwa da yin afuwa yayin da ake da ikon ramawa, siffofi ne da Allah yake sonsu, yake kuma ba da kyakkyawan sakamako idan an yi su. Haquri yana koyar da...