“Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba? Zariyat: 21
Nuna katika
“Lalle tsanani yana tare da sauqi” [Sharh: 6]
Alqur’ani yana tunatar da mutum wani abu da yake mantawa da shi yayin da yake tsaka a cikin wasu shagulgula: lallai tafiyar gajera ce...kuma ma’anar abu ta fi hayaniya muhimmanci.#Hasken_Alqur’ani#Mahanga#Tafiyar_rayuwa#Kofin_duniya#Musulunci
“Haqiqa Mun girmama ‘yan’adam”. [Isra: 70]
A gasar kofin duniya ana samun bambancin launukan mutane da yaruka da kuma garuruwa, sai dai kuma dukkanninsu suna nan a matsayin su na mutane ‘yan’adam.Don haka Alqur’ani yana tunatar da mu game da darajar kowane irin mutum.
Duk wata gasa da za a buga, to tana da manufa. To yanzu zai yiwu a hankalce rayuwar mutum ta zamo ba tare da wata manufa ba?
“Kuma an halicci xan’adam mai rauni ne”. [Nisa’i: 28]