Amana a Musulunci

Amana a Musulunci

Amana a Musulunci

92 39

Amana babban nauyi ce a Musulunci kuma kayan xauka ne masu nauyi. Abin da ake nufi da amana shi ne, bayar da haqqin Allah ta hanyar bauta masa da tsantsanta addini gare shi, da tsayuwa da haqqoqin halittu ba tare da tawaya ba. A Musulunci amana tana xaya daga cikin manyan turaku na gyaran xabi’a. Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi, ya qulla alaqa tsakanin amana da imani. Amana ta qunshi dukkan vangarorin rayuwar Musulmi na duniya da na lahira, tun daga abin da ya shafi ibadu, misali salla da azumi da zakka, zuwa abin da abin da ya shafi ayyukan gavovi, kamar ji da gani da zuciya. Hakanan ta qunshi rayuwa da dukiya da mace da ‘ya’ya da iyaye da maqota da cinikayya da wasiyoyi da shaidu da ayyukan qwadago da abin da ya shafi al’umma da ilimi. Allah Ta’ala yana cewa: “Lalle ji da gani da kuma tunani duk waxannan sun zama abin tambaya ne game da su”. Isra’i: 36]

Amana ta qunshi kiyaye addini da yaxa shi, da aiwatar da ibadu da ikhlasi da bin shari’a, da ba wa rai kulawa da tsarkaketa, da amfani da gavovi cikin abin da zai yardar da Allah. Kamar yadda kuma amana ta qunshi amfanar rayuwa cikin ayyukan xa’a, da yin mu’amala ingantacciya da kudi da tsayuwa da haqqoqin mace da ‘ya’ya da iyaye da maqota. Hakanan amana tana tsanantawa game da abin da ya shafi wajabcin cika alqawarin da aka yi wanda ya shafi cinikayya da yarjeniyoyi da zartar da wasiyoyi da adalci, da bayar da shaida da amana da tsayuwa da ayyukan da aka xora wa mutum da ikhlasi, da ba da kariya ga wurin da al’ummar Musulmi suke rayuwa da qarfafarsa, da xaukar ilimi da gaskiya da tsare sirrikan majalisa.

Kowane Musulmi yana xaukar nauyin amanar abin da aka amince masa a kansa, kuma da sannu Allah zai tambaye shi game da wannan amanar ranar alqiyama. Haqiqa Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi, ya tsoratar game da yin algus da ha’inci a amana, ya qarfafa zancensa da cewa, duk wanda bai kewaye abin da aka bashi kiwo da nasiharsa ba ba zai shaqi qamshin Aljanna ba. Amana ta tattaro kowane irin abu a rayuwa. Amana wani nauyi ne mai girma da Allah ya bijirar dashi ga sammai da qasa da duwatsu amma suka qi xauka, shi kuma mutum ya xauka

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya