Abin da ake nufi da ka zavi Allah shi ne, ka ‘yantu daga dukkan wani wanda ba shi ba.
#Tauhidi
Nuna katika
Yayin da zuciya ta cika da son Allah, dukkan wasu abubuwa da ake so za su zama ba wani abu ba, kuma ma’auni zai daidaita. #Son_Allah
Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne
Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu qauna
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulm
Shiriya tana farawa lokacin da zuciya ta fuskanto wa shiriya da gaskiya, ba lokacin da aka gama fahimta ba. #Shiriya
A duniyar da take cakuxe da duhu, Alqur’ani yana zuwa a matsayin wani haske da zai daidaita maka lamarinka, ba ma haka ba, sai ya nuna maka hanyar da za ka bi ka samu aminci. #Hanyoyin_Aminci