Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa’azi ga masu taqawa
Nuna katika
“Kaicona ina ma da ban riqi wane aboki ba!“Haqiqa ya vatar da ni daga bin Alqur’ani, bayan ya zo mini.” Shaixan kuwa ya kasance mai tavar da mutum neManzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa
Kowace aya ta sauka ne don isa zuwa ga zuciyarka... Kuma dukkan wani wa’azi da ke cikinsa ....kamar an rubuta shi ne don kai kadai. #Sako_Na Musamman
Idan watarana ka ji cewa kai kadai kana cikin duhu.. To ka tuna lallai fa Allah Majibinci ne, ba ya tozarta wanda ya fake dashi. #Allah_yana tare da kai
Idan ka samu zuciyarka a halarce a yayin karanta wata aya... To kana kusa da abin da kake tsammani #Ka saurara_da zuciyarka.
Duhu zai iya tsawaita a gareka.. Sai dai haske ba a nesa yake ba. Allah yana jibintar bayinsa...kuma yana fitar dasu zuwa ga haske. #Tafiyar_Haske
Alqur’ani ba ya zuwar maka da wani tunani da za ka warware shi, a’a sai dai shi kamar boyayyan sauti ne da yake raya abin da ka yi zaton ya mutu a zuciyarka. #Sautin_Alqur’ani