Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi; kuma Ya fari halittar mutum daga tavo
Nuna katika
Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi; kuma Ya fari halittar mutum daga tavo(7- AS-SAJDAH)
Haqiqa Mun girmama ‘yan’adam, Muka kuma xauke su (kan ababen hawa) na sarari da na ruwa, Muka kuma arzuta su daga tsarkakan (abubuwa) kuma Muka fifita su a kan wasu da yawa daga abin da Muka halitta nesa ba kusa ba
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?
Sannan idan aka gama salla sai ku bazu a bayan qasa ku kuma nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa don ku rabauta(AL‑JUMU‘AH-10)
Haqiqa kuna da kyakkyawan abin koyi tare da Manzon Allah, ga wanda yake yin kyakkyawan fata game da Allah da ranar lahira, ya kuma ambaci Allah da yawa(Suratul Ahzab-21)
Awo kuma a wannan ranar gaskiya ne. Don haka duk wanda ma’aunansa suka yi nauyi, to waxannan su ne masu rabauta(Suratul A’araf-8)